Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

Wani kudurin da zai hana zanen bille a fuska ya tsallake karatu na biyu a bainar, majalisar dattawa, bayan an tafka muhawara tsakanin yan majalisun da sauraron ra’ayoyin yan majalisar.

Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ne ya dauki nauyin wannan kuduri, wanda yayi ma taken “Kuduri dake da nufin samar da dokar haramta bille a fuska, tare da kamawa da gurfanar da duk wanda ya karyar dokar, shekara ta 2017”

KU KARANTA: Tsohon shugaban Gambia, Yahaya Jammeh ya koma gona

Yayin da ake tafka muhawara, Sanata Melaye yace ana yin zanen fuska ne da wuka ko aska, wanda hakan ke sanya mutum cikin halin jin zafi sosai, sa’annan kuma ba’a neman shawarar wadanda ake yi ma wa.

Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

Sanatoci sun ɗebo da zafi, sunyi dokar haramta ‘bille’ a fuska

A lokacin dayake jawabi, Melaye ya nuna ma abokan aikinsa hoton wani jariri yana ihu saboda zafin zanen da ake yi masa a fuska, daga nan sai ya roki sauran sanatoci dasu taimaka su mara ma wannan kudiri baya.

“Ina yin wannan bayani da bacin rai a tare dani, musamman idan na kalli hoton wannan yaron, sai inji hawaye na kwarara a idanu na. ina sanar da ku cewar a cikin mawuyacin hali ake yin wannan zanen fuska, inda ake amfani da wuka ko reza.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel