Kotun ta tsare manoma 3 a gidan yari a kan mutuwar wani makiyayi

Kotun ta tsare manoma 3 a gidan yari a kan mutuwar wani makiyayi

Kotu ta tsare manoma 3 a gidan yari bisa zargin kisan gilla da aka yi wa wani Fulani makiyayi.

Kotun majistare ta Makurdi a ranar Laraba, 22 ga watan Maris ta yanke hukuncin a kan wasu manoma 3 na kazance a gidan yari bisa zargin kisan gilla da aka yi wa wani Fulani makiyayi.

Kamfanin dilancin labarai ta Najeriya, NAN ta ruwaito cewa an gurfanar da monaman a kotu domin makircin aikata kisan kai.

Manoman da ake zargi ne Eric Tsambe, Agover Ioreren da Adua Terhile duk daga karamar hukumar Mbahimin Gwer ta gabas a jihar Binuwai.

'Yan sanda mai gabatar da kara, sufeto Ibrahim Akule, ya shaida wa kotun cewa wani malamin makarantar firamare na Mbahimin, Oralu Saawuan ya kawo karar a hedkwatar ‘yan sanda na Aliade a watan Fabrairu 28, 2017.

KU KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun raba kan su a manyan motoci 7, da Babura 40 a kusa da Magumeri, Borno

'Yan sanda sun cafke manoman da ake zargin aikata laifin a lokacin da suke gudanar da bincike.

Alkalin kotun majistare Mrs. Franca Yuwa ta dakatad da shari’ar har zuwa watan Mayu 9.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel