Yan Shi’a na zanga zanga a Abuja, sun bukaci a saki El-Zakzaky

Yan Shi’a na zanga zanga a Abuja, sun bukaci a saki El-Zakzaky

A ranar Laraba, 22 ga watan Maris, yan kungiyar musulman Shi’a sun mamaye unguwanni a babban birnin tarayya inda suka bukaci a saki shugaban su, Ibraheem El-Zakzaky, da matar sa, wadanda suka kasance a tsare tun watan Disamba 2015, duk da cewan kotu ta bada umurnin sakin su.

Yan kungiyar, wanda ko da yaushe suna sanye cikin bakaken kaya, sun yi zanga zanga mazan su da matan su a hanyar kasuwar Wuse Abuja.

Yan Shi’a na zanga zanga a Abuja, sun bukaci a saki El-Zakzaky

Yan Shi’a na zanga zanga a Abuja, sun bukaci a saki El-Zakzaky

Suna ta wakar : “Shugaban kasa, Ka saki shugaban mu"

"Ka bi umurnin kotu!"

"Ina adalcin ka!"

An kama Zakzaky da matar sa a ranar 14 ga watan Disamba, 2015, bayan wani karo tsakanin mambobin kungiyar sa da hukumar sojin Najeriya a Zaria, jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Mugun nufi: Yadda aka nemi a kashe shugaba Buhari

A kalla mutane 347 na kungiyar ne suka mutu bayan hukumar soji ta ce sun toshe babban hanya sannan suka hana shugaban hukumar, Tukur Buratai wuce wa.

Bayan an tsare sun a watanni ba tare da an kais u kotu ba, Zakzaky ya tunkari kotu inda ya bukaci a sake sa da matar sa.

A ranar 2 ga watan Disamba na shekarar bara, wata babban kotu dake Abuja karkashin jagorancin Justis Gabriel Kolawole yace ci gaba da tsare su ya saba ma doka.

Sannan kotun ta ba yan sanda umurnin basu masu tsaron sun a sa’oi 24 don kai su guri dake tsare.

Amma gwamnati ta yi watsi da umurnin inda ta ci gaba da tsare El-Zakzaky da matar sa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel