PDP ta sha kashi a Majalisar Wakilai

PDP ta sha kashi a Majalisar Wakilai

Wani Dan Majalisa a karkashin PDP ya tsere daga Jam’iyyar inda ya koma Jam’iyyar APC mai mulki. Hakan dai na karawa APC karfin rinjaye a Majalisar Tarayya

PDP ta sha kashi a Majalisar Wakilai

Kakaki da shugaban masu rinjayen Majalisa

Honarabul Hassan Anthony mai wakiltar Yankin Jihar Benue a Majalisar wakilai ta tarayya ya gudu ya bar Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin kasar a yau dinnan. Dan Majalisar ya sanar da sauyin shekar kafin a fara zaman Majalisa.

Nan take dai wani Dan Majalisar PDP daga Jihar Delta yace dole kakakin Majalisar ya bayyana cewa kujerar Dan Majalisar ta tashi aiki don kuwa ya sauya sheka. Shi dai Dan Majalisar yace rikicin Jam’iyyar PDP ta sa dole ya bar ta.

KU KARANTA: Za a nadawa Olusegun Obasanjo sarauta

An maida masa martani dai cewa babu wani rikici a PDP tun da Kotu ta bayyana Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban Jam’iyyar na hakika. Kakakin Majalisar dai ya takawa Dan Majalisar na PDP burki. Yanzu haka dai APC na da rinjaye a Majalisar.

Haka kuma Majalisar Dattawa tayi kira da Hamid Ali ya sauka daga kujerar sa na shugaban Hukumar kwastam na kasa. A jiya ne dai shugaban Hukumar kwastam na kasa Hamid Ali mai ritaya yace ba zai je Majalisar ba inda aka gayyace sa domin yayi bayani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel