Sheriff ya zargi Makarfi da bayar da cin ga Alƙalan kotun ƙoli

Sheriff ya zargi Makarfi da bayar da cin ga Alƙalan kotun ƙoli

Shugaban jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff ya zargi sanata Makarfi da shirya wata makarkashiya don siyan bakunan alkalan kotun koli, su bashu gaskiya a karar daya kai gabansu.

Sheriff ya zargi Makarfi da bayar da cin ga Alƙalan kotun ƙoli

Sheriff ya zargi Makarfi da bayar da cin ga Alƙalan kotun ƙoli

A baya dai kotun daukaka kara dake jihar Ribas ce ta yanke hukuncin cewar Sheriff ne halastaccen shugaban jam’iyyar PDP, hakan ne bai yi ma bangaren Makarfi dadi ba, inda ya garzaya gaban kotun koli.

KU KARANTA: Su wa suka fi kowa kudi a Najeriya?

Yayin dayake jawabi ga a madadin shugaban jam’iyyar PDP, mataimakinsa Cairo Ojougboh ya bayyana cewar sun samu labarin cewa tuni Makarfi ya kammala shirin biyan alkalan kotun cin hanci don su bashi gaskiya, Cairo ya zanta da manema labarai ne a shelkwatar jam’iyyar.

“Muna da tabbacin babu wanda ya isa ya siya alkalan kotun koli, kuma jam’iyyar mu nada cikakken yakini akan sabon alkalin alkalan kasar nan, mai shari’a Samuel Walter tare da abokan aikinsa.” Inji shi

Sai dai Kaakakin bangaren Makarfi Adeyeye Dayo yayi wuf ya musanta zargin Sheriff, inda yace wannan wani kokari ne da bangaren Sheriff din ke yin a ganin sun ci mutuncin alkalan kotun koli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel