Cin hanci da rashawa: Farfesa ya shaida ma kotu yadda ya baiwa ýan majalisa N50m, kuma sun karɓa

Cin hanci da rashawa: Farfesa ya shaida ma kotu yadda ya baiwa ýan majalisa N50m, kuma sun karɓa

Farfesa Benjamin Ogunbode tsohon daraktan cibiyar bincike tare da bada horo a harkar noma ya shaida mo kotu yadda wasu yan majalisu dake cikin kwamitin noma na majalisar wakilai suka nemi ya basu cin hancin N50m, kuamya basu.

Cin hanci da rashawa: Ferfesa ya shaida ma kotu yadda ya baiwa ýan majalisa N50m, kuma sun karɓa

Ferfesa Ogunbode

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito cewar tsohon daraktan ya bayyana ma wata kotu dake zamanta a garin Ibadan haka ne yayin daya gurfana gabanta akan tuhumarsa da ake da karkatar da miliyoyin nairori da suka kai N177m.

Farfesan ya kira sunayen wani dan majalisa mai suna Makanjuola wanda ke jagorantar wannan kwamiti a matsayin wanda ya amshi kudin daga hannun sa da kansa na sako ba, kuma N50m ya bashi. Sai dai Farfesan ya ki bayyana sunayen sauran yan majalisun da sanatoci da jami’an ma’aikatar kudi da suka rarraba N50m tsakaninsu wanda ya basu.

KU KARANTA: Wani Fasto dake haɗa bom yayi koƙarin tayar da bom a cocinsa

Ogunvode yace ya basu kudaden ne don yi musu godiya sakamakon kokarin da suka yi masa wajen sakar ma cibiyar dayake jagoranta a wancan lokaci kudaden gudanar da ayyukanta da suka kai N606m.

“Ni da kai na na mika wani dan majalisa mai suna Makanjoula kason su”, sa’annan Farfesan ya janye maganan da yayi a baya inda yace cibiyar daya shugabanta bata taba samun kudi daga hannun masu bada tallafi ba kamar yadda ya fada a baya, hakan ya sanya lauyan EFCC Rotimi Oyedepo ya shaida ma kotu lallai Farfesa ya sharara ma kotu karya kenan.

Shima alkalin kotun ya tabbatar da cewa Farfesa Ogunbode ya baiwa kotu takardu masu cin karo da juna, wannan ya nuna ba shi da gaskiya, amma lauyan Ogunbode ya musanta batun alkalin. Daga nan sai alkalin ya daga sauraron karar zuwa 17 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito a baya yadda hukumae EFCC ta gurfanar da Farfesa Ogunbode, Zachius Tejumola and Clement Adenose tun a shekarar 2014 inda take tuhumarsu da aikata manyan laifuka da suka shafi N177,571,609, wanda an samar da kudaden ne don biyan alawus alawus din ma’aikatan cibiyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel