Kwamishanan yan sanda yace sai an gurfanar da yaron gwamnan Nasarawa a Kotu

Kwamishanan yan sanda yace sai an gurfanar da yaron gwamnan Nasarawa a Kotu

Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da cewa ba da dadewa ba, za'a gurfanar da Khaleel, yaron gwamnan jihar Nasarawa a kotu kan laifin kisan kai.

Sai mun gurfanar da yaron gwamnan Nasarawa a Kotu - Yan sanda

Sai mun gurfanar da yaron gwamnan Nasarawa a Kotu - Yan sanda

Khaleel, haifaffen cikin gwamnan jihar Nasarawa, Alh Tanko Al Makura , ya bige wani dalibin makaranta, Amos Ovyeh, a daren ranan Lahadi lokacin da ya fita siyan batur.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa kwamishanan yan sandan jihar Nasarawa, Abubakar Sadiq Bello, yace za'a gurfanar da Khaleel a Kotu kan laifin kisan kai.

KU KARANTA: Naira ta kara daraja

“A iyakan sani na dai ,yaron da ake tuhuma na tsare a ofishin yan sanda kuma motarsa na hannun jami'an CID. Bayan an gudanar da bincike, za'a kaishi kotu."

A ranan litinin, an gudanar da zanga-zanga a Lafiya kan wannan al'amari. Wani idon shaidah ya ce su dai su ga wani direba yana wawan tuki.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel