Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Shugaban Hukumar Kwastam na kasa ya bayyana cewa aikin na sa aiki ne kuma babu wanda ya isa ya kawo matsala tun da shugaban kasa na tare da shi

Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Majalisa: Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Hamid Ali mai ritaya, shugaban Hukumar kwastam na kasa ya bayyana cewa shugaban kasa na tare da shi yana kuma goyon bayan aikin sa. Hamid Ali ne ya bayyanawa manema labarai wannan bayan ya fito daga Ofishin shugaban kasar a Fadar Villa.

Hamid Ali ya kuma bayyana cewa aikin na sa ba abu ne mai sauki ba tun farkon hawan sa har zuwa yanzu. Hamid Ali yace ya iske wasu manya ‘yan kasuwa da ke shigo da kaya daga kasar waje da suka yi kane-kane kan dokokin kasar.

KU KARANTA: Dala ta sha kasa a hannun Naira

Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Shugaba Buhari na tare da ni Inji Hamid Ali

Kanal Hamid Ali mai ritaya yace daga yanzu babu wanda ya isa gwamnati ta basa damar shigowa da kaya ba tare da ya biya ba kurum don yana cikin manya. Shugaban Kwastam din yace Najeriya na tafka mugun asara ta haka.

Jiya dai Hamid Ali ya rubuta takarda ga Majalisa inda ya bayyana mata cewa ba zai halarci gayyatar da tayi masa ba. Mun dai kuma samu labari cewa wata Kotu a Abuja ta haramtawa Majalisar damar gayyatan shugaban Kwastam din ya gurfana a gaban ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel