Ina tare da El-Rufai, shugaba Buhari da APC sun gaza - Bafarawa

Ina tare da El-Rufai, shugaba Buhari da APC sun gaza - Bafarawa

- Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce shi bai ga laifin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ba saboda ya rubuta wa shugaba Buhari wasikar gyara kayanka.

- A baya-bayan nan ne dai wata wasikar da Nasir El-Rufai ya rubuta wa shugaban Muhammadu Buhari, a watan Satumbar 2016, ta bayyana.

Ina tare da Elrufa'i, shugaba Buhari da APC sun gaza - Bafarawa

Ina tare da Elrufa'i, shugaba Buhari da APC sun gaza - Bafarawa

A cikin wasikar, El-Rufai ya nemi shugaba Buhari da ya yi karatun tanutsu wajen aiwatar da ayyukan alherin da jam'iyyar APC ta alkawarta wa al'ummar Najeriya.

KU KARANTA: Babbar magana: Yadda wasu suka so sakawa Buhari guba

Duk da wannan wasikar ta haifar da kace-nace a kasar, a inda wasu ma ke ganin beken Elrufa'i, shi kuwa Alhaji Bafarawa ya ce sam gwamnan na Kaduna ba shi da laifi.

Attahiru Bafarawa ya kuma kara da cewa tun da jam'iyyar PDP ta gaza, ya kamata ace APC mai mulki ta fitar da 'yan Najeriya daga halin da suke ciki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel