Yan ta'adda sanye da kayan sojoji sun kashe Fulani a Kaduna

Yan ta'adda sanye da kayan sojoji sun kashe Fulani a Kaduna

Rahotanni daga Kudancin jihar Kaduna sun nuna cewa wasu da ba a tabbatar ko jami'an tsaro ba ne sanye da kakin sojoji sun dira a wasu kauyuka da ake kira Kariyo da Dalle dake kusa da Jagindi, inda suka yi wa Fulanin yankin kisan kiyashi.

Yan ta'adda sanye da kayan sojoji sun kashe fulani a Kaduna

Yan ta'adda sanye da kayan sojoji sun kashe fulani a Kaduna

Lamarin wanda ya faru tun a yammacin ranar Litinin din da ta gabata, rahotanni sun nuna cewa sojijin sun kashe maza da suka hada yara da manya dake kauyukan. Daga cikin wadanda aka kashe har da Limami, Malamin Islamiyya da sauran matasa.

KU KARANTA: Barayin sun farma wata kasuwa a Arewa

A yayin jin ta bakin daya daga cikin mazauna yankin, ya tabbatar da cewa bayan sojojin sun kama wadannan mutane kafin su harbe su, sai da suka jibge su a cikin rana har zuwa karfe biyar na yamma kafin suka haura da su kan wani tsauni, inda suka bude musu wuta. Akalla an kashe kimanin mutane tara, inda kuma har zuwa yanzu ba a san inda saura suke ba.

Majiyarmu ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne a wani kauye da ake kira Aso duk a yankin na Jagindi, inda aka kashe wani Bafulatani a kan hanyarsa na kaiwa yaransa abinci a dajin da suke kiwo. Amma al'ummar yankin na Kariyo da Dalle sun yi mamaki yadda sojojin suka far musu duk da cewa ba su da alaka da rikicin na Aso.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel