Yawan dala a kasuwa ya tilasta darajar dala ta sauka zuwa N400 ga dala

Yawan dala a kasuwa ya tilasta darajar dala ta sauka zuwa N400 ga dala

Yawancin yan kasuwan canjin a Zone 4 Abuja da Legas sun dakatd da siyan dalar Amurka da ranan jiya saboda yawan dalan. Kwastamomin da ke zuwa kawai sayarwa suke basu siya, wannan abu kuma ya tayar musu da hankali.

Yawan dala a kasuwa ya tilasta darajar dala ta sauka zuwa N400 ga dala

Yawan dala a kasuwa ya tilasta darajar dala ta sauka zuwa N400 ga dala

Kana kuma wasu yan kasuwan na sauraron sakamakon tattaunawan zaman kwamitin kudi na babban bankin Najeriya CBN tayi jiya kafin su yanke kudin.

CBN ta kara dalar Amurkan da tuka cusawa kasuwan canjin daga $8,000 zuwa $15, 000.

Bayan ganawar kwamitin, CBN ta lashi takobin kulle tazarar da ke tsakanin kudin yan kasuwan canji da bankuna.

KU KARANTA: Ashe Dino Melaye karya yake, bai samu digiri a Havard ba

Yayinda gwamnan CBN, Godwin Emefiele ke magana da manema labarai bayan ganawar, yace Naira ta kara daraja a kwanakin nan sakamakon sakin dalar da bankin tayi.

Gwamnan kuma yace zau cigaba da yin hakan har sai an kulle tazarar kasuwan.

“Niyyarmu shine mu kulle tazarar da ke tsakani kamar dai yadda kuke gani kwanankin nan. Muna kyautata zaton cewa zamu kulle. Kuma zamu aiwatar da dukkan dokokin da ya kamata.”

“Mun yanke shawaran cewa akwai bukatan farfado da Naira a kasuwan canji kuma wannan ne dalilin da yasa muka fara daukan matakai, ina farin cikin cewa wadannan matakan da mua dauka sun fara haifan da mai ido, kuma zamu cigaba.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel