An tsinci gawar wani mutum ba kai ba wuya a jihar Sokoto (Hoto)

An tsinci gawar wani mutum ba kai ba wuya a jihar Sokoto (Hoto)

A ranar Littinin din da ta gabata ne yara 'yan jari Bola suka sami kansu a cikin tashin hankali a sanadiyar wani buhun da suke tsammanin kayan shara ce da suke iya samun wani abun saidawa don neman dan abin sawa bakin salati.

An tsinci gawar wani mutum ba kai ba wuya a jihar Sokoto

An tsinci gawar wani mutum ba kai ba wuya a jihar Sokoto

Abin ya faru ne a wata tulin shara akan titin Mai Tuta Road a cikin kwaryar birnin Sakkwato, bayan makarantar kwallejin Sarkin musulmi Abubakar(S.A.C)da safe.

'Yan jari bola sun ga buhun dake dauke da gawar, inda suna dagawa suka ga gawa ce, ta wani matashi amma an cire mata wuya da kai.

KU KARANTA: Majalisar dattijai zata kama da wuta

Wata majiya mai tushe, ta bayyanawa majiyar mu cewa sunan matashin Mujitaba. Kuma yana da matsalar tabin hankali. Sannan kuma dan unguwar Zoramawa ne dake bayan gidan Yari. Matashin dan shekaru 26 yana zama ne a cikin tashar motar Sakkwato a cewar majiyar.

An yi jana'izzarsa kamar yadda addinin musulunci ya yi umurni. Har zuwa yau ba'a gano masu hannu a wannan mummunan aiki ba.

Mai magana da yawun 'yan sandar jihar ASP Almustapha Sani ya tabbar da faruwar lamarin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel