Yau ce ranar ruwa ta duniya

Yau ce ranar ruwa ta duniya

- Yau ce ranar da majalisar dinkin duniya ta tsayar a matsayin ranar ruwa ta duniya

- An sayar da wannan ranar ne domin tunasar da al'ummar duniya muhimmancin samun tsaftataccen ruwa sha

Yau ce ranar ruwa ta duniya

Yau ce ranar ruwa ta duniya

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da a kan yi bikin Ranar Ruwa ta Duniya da nufin wayar da kan al'umma game da muhimmancin amfani da tsaftataccen ruwan sha.

A kowace shekara dai masu wannan bikin kan yi nazari kan wani maudu'i guda daya da ya shafi ruwa mai tsafta inda taken bikin na bana shi ne ''Dalilan da ke sa ake barnar ruwa''.

A shekarar 1993 ne aka fara bikin wannan rana, domin tunasar da al'ummar duniya muhimmancin samun tsaftataccen ruwa sha.

Yawanci dai kasashen masu tasowa na fama da matsalar samun tsaftataccen ruwa, wanda hakan ke jefa dumbin jama'a cikin mawuyacin hali kamar kamuwa da cutuka da dai makamantansu.

A Najeriya ma dai ana fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta, kuma rashin ruwa da muhalli mai tsaftar na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba a kasar.

Batun samar da ruwan matsala ce da jama'a da dama akasari daga yankunan karkara musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya suka dade suna fama da ita inda a wasu lokutan sukan bige da amfani da gurbataccen ruwa daga tafkuna.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka nemi a kashe shugaba Buhari

Masana sun dai yi hasashen cewar batun cimma burin samar da ruwan sha mai inganci da wadatuwa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel