Kamaru na ci gaba da korar 'yan gudun hijirar Nigeria

Kamaru na ci gaba da korar 'yan gudun hijirar Nigeria

- Kasar Kamaru ta kori mutane sama da 2,600 'yan gudun hijirar Najeriya daga kasar

- Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce, a na fama da rashin isasshen abinci da kuma rashin tsaro a kauyukan da aka komar da mutanen

Kamaru na ci gaba da korar 'yan gudun hijirar Nigeria

Kamaru na ci gaba da korar 'yan gudun hijirar Nigeria

Majalisar dinkin duniya ta ce Kamaru na tursasawa dubban 'yan gudun hijirar Najeriya daga kasar, wadanda rikicin Boko Haram yasa suka kaura da su koma gida.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce, ya zuwa yanzu, rundunar kasar ta mayar da sama da mutane 2,600 zuwa wasu kauyuka dake arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar ta ce kauyukan na fama da rashin isasshen abinci da kuma rashin tsaro.

A farkon watan nan ne kasashen biyu suka saka hannu a wata yarjejeniya dake cewa ba za a tilastawa 'yan gudun hijira komawa kasashensu ba.

Sama da 'yan gudun hijirar Najeriya 85,000 ne ke zama a yankin arewa mai nisa na Kamaru.

KU KARANTA KUMA: NSCDC sun kama mutane 2 da sun sata abinci gina jikin yara fakitoci 4,000 a Borno

A nan ne kungiyar Boko Haram ke yawan kai hare-haren da suke amfani da mata 'yan kunar bakin wake da kuma yara.

Hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, ya kuma raba dubun dubatar mutane da muhallinsu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel