Naira na cigaba da tashi sama

Naira na cigaba da tashi sama

Darajar Naira na ta kara tashi sannu a hankali a kasuwa. A jiya ma dai Naira ta yunkura a kan Dala Amurka da Dalar EURO ta Kasashen Turai.

Naira na cigaba da tashi sama

Naira na cigaba da tashi sama

A jiya Talata Naira ta yunkura a kan Dala Amurka da Dalar EURO ta Kasashen Turai kamar yadda rahotanni suka nuna. Nairar dai tayi wani mugun tsalle inda ta haura matakai har N15. Yanzu dai Dalar Amurka ta koma N430 daga kan N445.

Haka kuma dai Nairar ta daga a kan Dalar EURO wanda ta koma N450 daga kan N465. Sai dai Nairar ba ta motsa ba ko kadan a kan Pounds Sterling na Kasar Ingila wanda har yanzu yake nan a kan N530 kan kowane Pound guda.

KU KARANTA: Har yanzu 'Yan Najeriya na kaunar Buhari

Naira na cigaba da tashi sama

Naira na cigaba da tashi sama

Hakan na zuwa ne dai bayan da babban bankin kasar watau CBN ta kara sakin wasu makudan Daloli a kasuwa ga masu sayen wasu kayan sari da kuma zuwa kasashen waje domin karatu ko rashin lafiya.

Dama can babban bankin Najeriya CBN ta ce kashin Dala ya bushe a wannan makon don kuwa za ta cigaba da sakin miliyoyin daloli domin a biya bukatar jama’a. Masu canji dai sun ce hakan ya taimaka wajen gyara lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba a wurin bincike akan cin hancin naira 50

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel