Abin da ya sa Hamid Ali ba zai bayyana gaban Sanatoci ba

Abin da ya sa Hamid Ali ba zai bayyana gaban Sanatoci ba

Shugaban Hukumar Kwastam na kasa Hamid Ali ya fadawa Majalisa dalilin da ya hana sa zuwa Majalisa. Yace bari ma dai ba zai kara zuwa ba ko da an gayyace sa.

Abin da ya sa Hamid Ali ba zai bayyana gaban Sanatoci ba

Hamid Ali ba zai bayyana gaban Sanatoci ba

Hamid Ali ya rubuta takarda jiya ga Majalisa inda ya bayyana mata cewa ba zai halarci gayyatar da tayi masa ba. Mun dai kuma samu labari cewa wata Kotu a Abuja ta haramtawa Majalisar damar gayyatan shugaban Kwastam din ya gurfana a gaban ta.

Kotu ta bayyana cewa Majalisa ba ta da hurumin ta fadawa Hamid Ali shugaban Kwastam aikin sa don kuwa shugaban kasa ne ya nada sa. Dama can wani babban Lauya da aka sani Femi Falana yace shiga-sharo-ba-shanu ne kurum Majalisa ta yi.

KU KARANTA: Kotu ta hana Sanaotci kiran Hamid Ali

Abin da ya sa Hamid Ali ba zai bayyana gaban Sanatoci ba

Hamid Ali yace ba zai bayyana gaban Sanatoci ba gaba daya

Tun can dai Kanal Hamid Ali mai ritaya ya bayyana cewa ba zai je gaban Sanatocin ba kamar yadda yace ya gana da Ministan shari’a na kasa wanda ya ba sa wannan shawara. Majalisar dai ta kora Hamid Ali wancan makon inda tace ya koma ya sa rigar sa shi kuma ya tubure.

Har ila yau an kuma fara binciken shugaban Majalisar Bukola Saraki. Ana zargin Bukola da yin ba dai-dai ba wajen shigo da wata mota kirar Range Rover wanda tuni dai Hukumar Kwastam ta karbe ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel