Rikici: Yaki zai barke a Majalisar Dattawa

Rikici: Yaki zai barke a Majalisar Dattawa

Daga Hamid Ali na Kwastam zuwa Ibrahim Magu. Akwai dai rikici-rikice iri-iri da ake ta fama da shi a Majalisar Dattawar Najeriya. Ko ya za a kare wannan karo. Oho!

Yaki zai barke a Majalisar Dattawa

Yaki zai barke a Majalisar Dattawa

A jiya ne dai shugaban Hukumar kwastam na kasa Hamid Ali mai ritaya yace ba zai je Majalisa ba gaba daya. Hamid Ali ya bayyana haka ne bayan yace ya gana da Ministan shari’a na kasa Abubakar Malami SAN.

Majalisar dai ta kora Hamid Ali wancan makon inda tace ya koma ya sa riga, ya kuwa ce bai ga inda dokar da ta tilasta masa ba. Haka kuma Sanatoci sun ce sun dauki matakin karshe game da Ibrahim Magu na EFCC. Majalisar ta ki amincewa ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC shi ma a makon jiya. Yanzu dai ana jiran martanin shugaban kasa.

KU KARANTA: Hamid Ali: Kotu ta takawa Majalisa birki

Rikici: Yaki zai barke a Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa: Za a binciki Saraki da Melaye

Har ila yau kuma za a fara binciken shugaban Majalisar Bukola Saraki da kuma Sanata Dino Melaye. Ana zargin Saraki da yin ba dai-dai ba wajen shigo da wata mota, yayin da Jaridar Sahara Reporters ta taso Dino Melaye a gaba inda tace bai yi mafi yawancin karatun da yake cewa yayi ba.

A jiya dai bayan da Bukola Saraki ya bar Majalisar zuwa Kotu domin cigaba da shari’ar sa ne Sanata Ali Ndume ya kawo kudirin cewa a binciki Sanatocin. Sanata Ike Ekweremadu da ke jagorantar zaman ya kuwa yi na’am da maganar. Tuni dai har Sanata Dino Melaye ya fara maida martani ga Ali Ndume inda ya kira sa dan Boko Haram.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel