Dino Melaye ya caccaki Ali Ndume akan takardan makaranta

Dino Melaye ya caccaki Ali Ndume akan takardan makaranta

- Sanata Dino Melaye ya jaddada cewa ya karashe karatunsa a jami’ ar Ahmadu Bello

- An samu rahotannin cewa bai karashe karatunsa a jami’ar ba

- Majalisar dattawa na gudanar da bincike cikin al’amarin

Dino Melaye ya caccaki Ali Ndume akan takardan makaranta

Dino Melaye ya caccaki Ali Ndume akan takardan makaranta

Sanata Dino Melaye ya caccaki Sanata Ali Ndume akan bukatar da yayi ne cewa majalisar dattawa tayi bincike kan tuhumar cewa bai karashe karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello ba.

Jaridar SaharaReporters ta samu labarin cewa duk da cewa Dino Melaye yayi karatu a jami’ar, bai karashe karatunsa ba

Sanata Ali Ndume a yau Talata, 20 ga watan Maris, ya bukaci majalisar dattawa ta gudanar da bincike cikin al’amarin.

Shi kuma Melaye ya mayar da martani ga Ndume inda yace masa dan Boko Haram.

Yace: “ Na zo domin raddi kan maganar da wanda ake zargi da Boko Haram kuma sanata, Ali Ndume. Wannan ba matsala bane. A fahimta ta cigaba b. a demokraiyya , babu sanatan da yafi karfin a bincikesa kuma a karshe, gaskiya zata bayyana.

“Maganan cewa ban karashe karatuna a jami’ar ABU ba Kaman cewa ni ba sanata bane.”

“Ina mai sanar da cewa wannan digiri da nike yi yanzu, na takwas ke. Nayi karatu a jami’ar Abuja, nayi a makarantan kasuwanci da siyasa a Landan. Kana kuma nayi karatu a jami’ar Harvard.”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel