‘Har yanzu yawancin ýan Najeriya na ƙaunar shugaba Buhari’ – inji fadar shugaban ƙasa

‘Har yanzu yawancin ýan Najeriya na ƙaunar shugaba Buhari’ – inji fadar shugaban ƙasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cika alkawurran daya daukan ma yan kasa, musamman ta bangaren habbaka tattalin arziki, samar da ayyuka, da kuma tsaron rayuka da dukiyoyi.

‘Har yanzu yawancin ýan Najeriya na ƙaunar shugaba Buhari’ – inji fadar shugaban ƙasa

‘Har yanzu yawancin ýan Najeriya na ƙaunar shugaba Buhari’ – inji fadar shugaban ƙasa

Kamar yadda fadar shugaban ta bayyana, yawancin jama’an Najeriya na jin dadin yadda shugaba Buhari ke tafiyar da gwamnatinsa, kuma sun yi amanna da kamun ludayinsa, inji rahoton Vanguard.

KU KARANTA: YANZU YANZU: Majalisar dattawa ta fara binciken Melaye

Mashawarcin shugaba Buhari kan fannin watsa labarai Femi Adesina ne ya shaida haka yayin dayake tarbar kungiyar matasan Arewa masu karajin tabbatar da zaman lafiya da shugabanci na gari a garin Abuja.

Adesina yace: “Ina mai farin ciki ta yadda har yanzu yawancin yan Najeriya suna tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman yadda naga jama’a ke nuna farin cikinsu da dawowarsa daga birnin Landan, hakan tabbaci dake nuna irin soyayyar da kuma amanna da yan Najeriya su kayi da shugabancin shugaba Buhari

“An fara samun juyi mai kyau a bangaren tattalin arzikin kasa, yaki da cin hanci da rashawa, aikin noma, samar da ayyukan yi, kuma ina mai tabbacin cewa shugaba Buhari zai kai Najeriya ga gaci kafin shekarar 2019.”

Kungiyar matasan Arewan sun karrama Adesina da lambar yabo na iya shugabanci, shima Adesina ya gode ma matasan, kuma ya bayyana cewar mutunci da dattakun shugaba Buhari ne ya bashi kwarin gwiwar bada gudunmuwarsa a gwamnatin.

Shugaban kungiyar, Kwamared Muhammadu Abubakar ya bayyana Adesina a matsayin kifin zinari, wanda ba zai iya boyuwa ba.

“Matasan Arewa a karkashin kungiyar matasan Arewa masu karajin tabbatar da zaman lafiya da shugabanci na gari mun karramaka da sarautan ‘Garkuwan matasan Arewa’ saboda gudunmuwar da kake baiwa matasa” inji Kwamared

A wani hannu kuma, ministan kudi Kemi Adeosun tace gwamnatin tarayya zata duba korafin gwamnatin jihohi dangane da kudaden biyan bashi na Paris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel