Rikicin majalisa da shugaban kwastam: Hamid Ali ya ruga fadar shugaban ƙasa

Rikicin majalisa da shugaban kwastam: Hamid Ali ya ruga fadar shugaban ƙasa

Tirka tirkan tsakanin majalisar dattawa da shugaban hukumar kwastam laftanar kanar Hamid Ali mai murabus kan batun sanya kakin jami’an hukumar yaki ci yaki cinyewa.

Hakan ne ya sanya shugaban hukumar Hamid Ali ya ruga fadar shugaban kasa a ranar Talata 21 ga watan Maris, inda ya tsegunta ma yan jaridu cewar ba zai amsa gayyatar majalisar ba, kamar yadda ta bukace shi daya gurfana gabanta a ranar Laraba 22 ga watan Maris.

Rikicin majalisa da shugaban kwastam: Hamid Ali ya ruga fadar shugaban ƙasa

Rikicin majalisa da shugaban kwastam: Hamid Ali ya ruga fadar shugaban ƙasa

Hamid Ali ya bayyana hakan ne a daidai lokacin daya fito daga masallacin fadar shugaban kasa inda yayi sallan Azahar.

A ranar Alhamis din data gabata ne majalisar ta umarci shugaban kwastam din daya gurfana gabanta sanye da cikakken kakin jami’an hukumar kwastam din a ranar Laraba 22 ga watan Maris, sai dai tun a lokacin ne Hamid Ali ya shaida ma majalisar cewa shi fa bai ga wata doka data tilasta masa sanya kakin jami’an hukumar ba.

KU KARANTA: Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?

Sai dai cikin raha, Hamid din ya shaida ma yan jaridun fadar shugaban kasa cewa kaftani ne kakinsa, sa’annan ya kara da cewa ba zai samu daman gurfana gaban majalisa ba dangane da sammacin daya smau daga wat kotu, don haka, amsa gayyatan majalisan ka iya zama tamkar yin karan tsaye ne ga kotu.

Hamid yace: “Tuni wani lauya ya kai maganan gaban kotu, kuma na samu sammacin shigar damu kara kotu da lauyan yayi, don haka rashin yi ma kotu biyayya ne muddin na gurfana gaban majalisar, don haka zan dakata kuma in tsumayi hukuncin kotun.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel