Jami’an yansanda sun kama gwanin satan waya a masallaci

Jami’an yansanda sun kama gwanin satan waya a masallaci

Jami’an hukumar yansandan jihar Osun sun samu nasarar cafke wani matashi mai shekaru 24 Olatunde Rahman da laifin satar waya a masallatai.

Jami’an yansan da sun kama gwanin satan waya a masallaci

Jami’an yansan da sun kama gwanin satan waya a masallaci

Hukumar yansanda ta gurfanar da barawon wayoyin gaban kuliya manta sabo, inda dansanda mai shigar da kara Fagboyinbo Abiodun ya bayyana ma kotu cewar Olatunde ya kutsa kai cikin masallacin Kosemani a ranar 17 ga watan Maris, inda ya saci manyan wayoyi guda 4 da na’urar tafi da gidanka guda daya.

KU KARANTA: Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?

Jami’an yansanda sun kama gwanin satan waya a masallaci

Jami’an yansanda sun kama gwanin satan waya a masallaci

Dansandan ya shaida ma kotu cewar wayoyin mallakin wasu dalibai ne da suka hada da Bolarinwa Adekunle, Adetola Mubarak, Aderanti Adedotun da Usman Suliyat, kuma sun makala su caji ne a cikin masallacin sa’adda Olatunde ya lallabo ya sace su.

Bugu da kari an shaida ma kotu cewa duk a rana daya, Olatunde ya tsallka dakin wani mai suna Rafiu Saheed da wani Sunday Victor, inda suma ya sace musu wayoyi. Dansanda mai kara ya shaida ma alkalin kotun cewa laifukan da ake tuhumar Olatunde dasu sun saba ma sashi na 390 (9), 412, 415 da na 516 na kudin hukunta laifuka.

Da aka karanto masa laifukansa, Olatunde ya musanta duka, inda lauyansa ya roki kotu data bada belin wanda yake wakilta

Daga karshe Alkalin kotu, mai shari’a Olusola Aluko ya bada belin Olatunde kan kudi N100,000, sa’annan y adage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Afrilun 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel