‘Dalilin daya sa ba zan gurfana gaban majalisar dattawa ba’ – inji shugaban kwastam

‘Dalilin daya sa ba zan gurfana gaban majalisar dattawa ba’ – inji shugaban kwastam

Shugaban hukumar hana fasa kauri ta kasa da aka fi sani da suna Kwastam ya bayyana cewa ba zai gurfana gaban majalisar dattawa ba a ranar Laraba 22 ga watan Maris kamar yadda suka umrce shi ba.

Ali ya tabbatar da haka ne a wata ganawa da yayi da manema labaru a ranar Talata 21 ga watan Maris a garin Abuja.

Hamid Ali ya bayyana dalilansa na kin hallara gaban majalisar da cewa ya samu wani sammaci daga wani lauya daya shigar da kara gaban kotu, don haka yi ma kotu karan tsaye ne idan ya gurfana gaban majalisar a gobe musamman dangane da batun sanya kakin hukumar kwastam wande shine batun da ake tuhumarsa a kai a gaban kotun.

KU KARANTA: Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?

Ali yace “Duba da shawarwarin da lauyoyi suka bani, da kua bayanai dana samu daga ofishin babban lauyan gwamnati, ba zan gurfana gaban majalisa a gobe ba, har sai kotu ya yanke hukunci.”

Ali ya cigaba da bayaninsa, inda yace aikin hana fasa kauri da suke yi ya hana manyan mutane masu shigo a motoci cin karensu babu babbaka, ba tare da biya musu haraji daya kamace su ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel