Buhari yayi Allah wadai da kashe kashen mutane da ake yi, ya jajanta ma jama’an Binuwe

Buhari yayi Allah wadai da kashe kashen mutane da ake yi, ya jajanta ma jama’an Binuwe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma gwamnati tare da jama’a jihar Binuwe sakamakon hare haren da aka kai a wani kasuwa dake garin Zaki Biam, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Buhari yayi Allah wadai da kashe kashen mutane da ake yi, ya jajanta ma jama’an Binuwe

Buhari yayi Allah wadai da kashe kashen mutane da ake yi, ya jajanta ma jama’an Binuwe

Shugaban kasa yayi tir da wannan harin, kuma ya umarci jami’an tsaro dasu gudanar da binciken gaggawa don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki, tare da ganin an hukunta su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma wadanda suka rasa yan’uwansu sakamakon harin, kuma yayi addu’ar Allah ya basu hakurin juriya.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Bugu da kari shugaban yayi Allah wadai da ireiren hare haren da ake kaiwa a sauran sassan kasar nan, inda ya kalubalanci hukumomin tsaro dasu tashi haikan wajen gudanar da aikinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.

“Ya zama wajibi a garemu da mu yi tir da yawan kashe kashen jama’a da ake yi a kasar nan, da alama mun yi watsi da koyarwar addinan mu na girmam ran mutum, mu sani babu wanda ke da hurumin daukan ran da bai halitta ba,” inji Buhari.

Daga karshe shugaba Buhari ya bukaci yan kasa dasu zauna lafiya da juna tare kaunar juna, sa’annan kada su bari rashin jituwa ya janyo rikicin da zai janyi asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel