Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Wani abin mamaki mai daukan hankula ya faru a kasar Sin wato China, inda wata mata tayi watsi da kudadenta da yawansu ya kai N725,000.

Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Sai dai yayin da take watsi da kudaden nata, sai jama’a suka koma gefe suna kallo cikin mamaki, har sai da yansanda suka iso wurin suka kwashe kudaden, sa’annan suka shiga neman mai su.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Abinka da kasashen da aka cigaba, ashe na’urar daukan hoto na kan titi ya dauki hoton matar, ta haka ne yansandan suka iya gano ta, har suka kai mayar mata da kudin nata, inda ta bayyana musu cewa ran ta ne y abaci, shi yasa ta zubar da kudin.

Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Fushi ya tunzura wata mata ta watsar da kudinta N725,000, tayi da na sani

Wannan lamari ya faru ne a birnin Chongqing, lamarin har sai daya haifar da cunkoson ababen hawa, kuma wani karin mamaki shine yadda jama’an dake wajen kowa ya koma gefe yana kallon ikon Allah, babu wanda ya kai ma kudaden hari, da haka ne yansandan suka iya gano kudaden gabaki daya.

Yansanda sun bayyana siffar matar da cewa: “Tana da gashin mai tsawo, tana sanye da rigar sanyi da gajeren wando,” sai dai jama’a sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani cikin raha yace: “Zan so in dinga kasancewa dake a duk lokacin da kike cikin fushi,” wani kuma yace: “Gaskiya raina ya baci bayan karanta labarin nan, saboda ko N725,000 din ma bani da shi.”

Ga bidiyon matan nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel