Amurka za ta hana kasashe Musulmai 8 shiga jirgi da kwamfuta (Kalli kasashen da abun ya shafa)

Amurka za ta hana kasashe Musulmai 8 shiga jirgi da kwamfuta (Kalli kasashen da abun ya shafa)

Gwamnatin Trump ta tabbatar da cewa zata haramtawa wasu kasashe takwas na yankin Gabas ta Tsakiya da Kudancin Afirka, shiga jirage masu zuwa kasar da kayayyakin wuta irin su kwamfuta.

Amurka za ta hana kasashe Musulmai 8 shiga jirgi da kwamfuta (Kalli kasashen da abun ya shafa)

Amurka za ta hana kasashe Musulmai 8 shiga jirgi da kwamfuta (Kalli kasashen da abun ya shafa)

Amurka za ta haramtawa wasu kasashe takwas na yankin Gabas ta Tsakiya da Kudancin Afirka, shiga jirage masu zuwa kasar da kayayyakin wuta irin su kwamfuta.

Wata majiya daga gwamnatin Amurka ta shaida cewa, matakin zai shafi kamfanin jirage guda goma ne wadanda suke jigila a filayen jiragen saman kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni na kokarin karkatar da kudin da shugaba Buhari zai aika masu

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, an dauki wannan mataki ne saboda bayanan sirri da aka samo daga wasu kasashe.

An kuma ruwaito cewa matakin zai hada ne da haramta shiga da kayayyaki kamar kwamfutoci da kyamarori da na'urar bidiyo ta DVD da na'urar yin gem, amma ban da wayoyi.

Filayen jirgin sama da abun ya shafa sune na Amman, Cairo, Kuwait, City, Doha, Dubai, Istanbul, Abu Dhabi, Casablanca, Morocco; Riyadh da Jedda, Saudi Arabia.

Hukumar kula da tsaron cikin gida ta Amurka, ta ki cewa komai a kan lamarin, amma ana sa ran za ta gabatar da jawabi a ranar Talata.

Ita ma hukumar Tsaro ta bangaren Sufuri ta ki tofa komai kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Majalisar dattawa ta fara binciken Melaye

Jami'ai sun ce matakin ba shi da ranar karewa. Kamfanin AP ya ruwaito cewa ba a sanar da kamfanin jiragen saman a hukumance ba har sai da misalin karfe bakwai na safiyar Talata.

Sai dai kamfanin jirgin sama na Jordan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, zai haramtawa fasinjoji shiga jiragensa masu zuwa Arewacin Amurka da kayan lantarki, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta fara ruwaitowa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel