Babban Bankin Najeriya na ci gaba da malalo dala

Babban Bankin Najeriya na ci gaba da malalo dala

Labarin da muke samu yanzu yana nuna cewa darajar Naira na ci gaba da dagawa sama yayin da shi kuma babban bankin Najeriya yake ci gaba da malalo dala a kasuwannin canjin.

Babban bankin Najeriya na ci gaba da malalo dala

Babban bankin Najeriya na ci gaba da malalo dala

A yau dai munsamu labarin cewa ana saida Dala 1 ne akan N415 a kasuwannin bayan fage. wannan dai yana zuwa ne bayan da babban bankin kasar Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) yake ci gaba da zuba kudin dala din a bankuna da kuma kasuwannin cancin.

A jiya ma dai Jaridar NAN ta bada rahoton cewa kudin Najeriya ta kara daraja a kasuwan bayan fagge.

Yan kasuwan canji sun nuna farin cikinsu ga yadda abubuwa suke gudana a yanzu kuma suna kara kira ga babban banki CBN ta rage bambancin da ke tsakanin bankuna da kasuwan bayan fagge.

KU KARANTA: Ku kalli fuskokin wadanda suka haddasa kisan Hausawa a Ile Ife

A bangare guda, Farfesa Sherifdeen Tella, wani masanin tattalin arziki a jami’ar Olabisi Onabanjo, jihar Ogun, yace cusa dala kasuwan canji ba zai fishemu ba.

Yace: “Bana tunanin cusa dla kasuwan canji wata mafita ce na din-din-din ga kalubalen canji. Kawai dai ana yi ne."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel