Wani Gwamna zai gina hanyoyi na kilomita 500

Wani Gwamna zai gina hanyoyi na kilomita 500

Gwamnan Jihar Kano Mai grima Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fara shirin gina hanyoyi har na kilomita 500 a fadin Jihar Kano

Gwamna Ganduje

Gwamna Ganduje zai gina hanyoyi na kilomita 500

Mai Girma Gwamna Abdullahi Ganduje zai gina tituna har na tsawon kilomita 500 a kauyukan Jihar Kano. Hakan zai taimaka wajen jigilar jama’a da kayan gona da kasuwanci da sauran su tsakanin Kauyuka na Jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne dai ya sanar da wannan da kan sa lokacin da ya kaddamar da shirin hanyar Garun Malam zuwa Kwiwa har Agalawa cikin ‘yan kwanakin nan a karamar Hukumar Garun Malam din.

KU KARANTA: Za a rage kudin jarrabawar WAEC

Gwamna Ganduje

Gwamna Ganduje zai gina hanyoyi a Kauyukan Kano

Dr. Ganduje ya sa wa shirin suna ‘Karkara Salamu Alaikum’. Gwamnan yace akwai bukatar a gina tituna har na kilomita 1000 a Jihar Kano domin sha’anin makaranta da asibiti da sauran al’amura na yau da kullum. A karshen Gwamnan yace mutanen Kano ne dai za su yi aikin.

Wani tsohon Soja yace Gwamnoni har sun fara kutun-kutun din ganin yadda za su yi gaba da kudin da Gwamnatin Tarayya za ta saki ga Jihohi har Naira Miliyan 500. Don haka yace ayi maza a dakatar da shirin

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel