Lema ta yage a jihar Nasarawa, jiga-jigai 2 sun koma APC

Lema ta yage a jihar Nasarawa, jiga-jigai 2 sun koma APC

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa kuma yan majalisar dokokin jihar da suka hada da Ibrahim Alkali da mataimakin mai tsawatar wa a majalisar Muhammad Muluku sun sauya sheka ya zuwa APC.

Lema ta yage a jihar Nasarawa, jiga-jigai 2 sun koma APC

Lema ta yage a jihar Nasarawa, jiga-jigai 2 sun koma APC

Kakakin majalisar jihar mai suna Ibrahim Balarabe shine ya sanar da hakan a zaman majalisar da ya gabata yana mai taya su murna da hukuncin da suka daukar wa kansu da kansu.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Majalisa zata fara binciken Saraki da Dino Melaye

Daga nan ne kuma sai kakakin ya tabbatar masu da cewa tabbas ba za'a nuna musu bambancin ba a cikin jam'iyyar ta APC.

Tun farko dai, wadanda suka sauya shekar sun bayyana rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a matakin kasa shine ummulhaba'isin barin jam'iyyar ta su ta PDP.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel