‘Ya kamata a rage kudin zana jarabawar WAEC’ inji Minista

‘Ya kamata a rage kudin zana jarabawar WAEC’ inji Minista

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya bukaci hukumar zana jarabawa ta WAEC dasu duba yiwuwar rage kudin yin rajistan zana jarabawar don sama ma dalibai sauki.

‘Ya kamata a rage kudin zana jarabawar WAEC’ inji Minista

Minista Adamu Adamu

Ministan ya bayyana haka ne yayin dayake maraba da shuwagabannin hukumar WAEC da suka kawo masa ziyara a karkashin jagorancin shugaban hukumar Evelyn Kandakai.

Minista Adamu yace iyaye da dama suna korafi dangane da tsadar kudin jarabawar, wanda hakan ke zamo tarnaki da iyayen da daliban, har ta kai ga yaran basa samun daman zana jarabawar.

KU KARANTA: Kaakakin majalisa da ýan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Shima karamin ministan ilimi Anthony Anwukah ya yaba ma WAEC a bisa gudunmuwar da suke baiwa wajen cigaban kasashen yammacin Afirka, kuma ya bukaci shugaban WAEC da tayi amfani da damanta wajen zamowa abin koyi ga yan mata don su samu kwarin gwiwar yin karatu.

A nata jawabin, Kandakai ta jinjina ma Najeriya a bisa gudunmuwar da take baiwa hukumar WAEC a tsawon shekaru da dama.

An samar da WAEC ne a shekarar 1951, kuma suke shirya jarabawar kammala sakandari a kasashen yammacin Afirka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel