Dalilin da yasa yan arewa ke zaune cikin talauci – Shehu Sani

Dalilin da yasa yan arewa ke zaune cikin talauci – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa talauci ke ci gaba da yaduwa a yankin arewacin Najeriya duk da yawan manyan mutane da yankin ke takama da su.

Dalilin da yasa yan arewa ke zaune cikin talauci – Shehu Sani

Shehu Sani ya ce shugabannin arewa su zamo nagari abun koyi

A cewar sanatan dake wakiltan jihar Kaduna ta tsakiya, yawancin mutanen arewa na zaune cikin gurkumin talauci ba wai don kawai sun kasance malalata ba, amma saboda wadanda keda arziki a yankin kan su kawai suka sani.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni na kokarin karkatar da kudin da shugaba Buhari zai aika masu

Ya kuma zargi jihohin yankin da dogaro ga gwamnatin tarayya kan kudaden wata-wata.

Sanatan wanda yayi magana a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar mata na Women Connect Initiatives (WCI) a ofishin sa dake Abuja, ya bukaci gwamnonin jiha a yankin da su yi aikin mai kyau da za’ayi koyi da su sannan kuma su daina yawan dogaro a kan cibiyar gwamnati.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel