Kash: Dangote ya sullubo daga jerin masu kudin Duniya

Kash: Dangote ya sullubo daga jerin masu kudin Duniya

– Alhaji Aliko Dangote mai kudin Najeriya ya sauka daga jerin Attajirai 100 na Duniya

– Yanzu Dangote ne mutum na 105 a masu kudin Duniya

– Amma duk Afrika dai Dangote bai da tsara

Aliko Dangote na cikin masu kudin Duniya

Dangote ya sullubo daga jerin masu kudin Duniya

Rahotanni da ke fitowa daga Forbes wannan shekarar sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya fita daga cikin sahun mutane 100 da suka fi kowa kudi a Duniya. A wannan shekarar ne Dangote ya sullubo daga jerin bayan da kuwa yana ciki.

Yanzu haka Alhaji Dangote ne mutum na 105 a masu kudin Duniya kaf. Dangote dai shekarun sa 59 ne rak amma ya mallaki wannan makudan kudi. Rugurgujewar tattalin arzikin da Najeriya ta shiga ne dai ya taba Dangote.

KU KARANTA: Izala za ta bude cibiyoyin koyan sana'a

Alhaji Aliko Dangote ya mallaki makudan kudi sama da Biliyan 12 inda yake da Kamfuna kuma a Kasashen Sanagal, Kamaru, Zambia, Ghana, Togo, Tanzania, Zambia, Afrika ta kudu da sauran su. Duk Afrika dai ba mai kudin Dangote.

Jaridar Forbes ta bayyana cewa arzikin mai kudin Najeriya da ma Afrika Alhaji Aliko Dangote ya fi abin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mallaka. Dangote dai ya taba shigowa cikin sahun mutane 25 da suka fi kowa arziki a Duniya shekaru 3 da suka wuce.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel