Naira ta kara daraja a kasuwan canji a yau Litinin

Naira ta kara daraja a kasuwan canji a yau Litinin

Jaridar NAN ta bada rahoton cewa kudin Najeriya ta kara daraja a kasuwan bayan fagge a yau Litinin, 20 ga watan Fabrairu.

YANZU-YANZU : Naira ta kara daraja a kasuwan canji a yau Litinin

YANZU-YANZU : Naira ta kara daraja a kasuwan canji a yau Litinin

Kudin Najeriya ta kara daraja inda aka sayar da ita N445 ga Dalar Amurka sabanin N450 da aka sayar a ranan Juma’a.

Amma a kasuwan canji wato Bureau De Change (BDC) anyi canjin Naira N398 kuma ana sayarwa N400.

KU KARANTA: An kama wata mata da laifin jefa jariri masai

Yan kasuwan canji sun nuna farin cikinsu ga yadda abubuwa suke gudana a yanzu kuma suna kara kira ga babban banki CBN ta rage bambancin da ke tsakanin bankuna da kasuwan bayan fagge.

A bangare guda, Farfesa Sherifdeen Tella, wani masanin tattalin arziki a jami’ar Olabisi Onabanjo, jihar Ogun, yace cusa dala kasuwan canji ba zai fishemu ba.

Yace: “Bana tunanin cusa dla kasuwan canji wata mafita ce na din-din-din ga kalubalen canji. Kawai dai ana yi ne."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel