Kungiyar Izala zata gina cibiyar koyar da sana’o’i

Kungiyar Izala zata gina cibiyar koyar da sana’o’i

A kokarinta na inganta rayuwar al’umma, kungiyar Jama’atul Izalatul bidi’a wa iqamatissunnah, JIBWIS wanda aka fi sani da suna Izala ta kammala shirye shiryen samar da cibiyar koyar da sana’o’i a duk fadin kasar nan.

Kungiyar Izala zata gina cibiyar koyar da sana’o’i

Kungiyar Izala zata gina cibiyar koyar da sana’o’i

Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana haka yayin dayake ganawa da yan jaridu a jihar Gombe, a ranar Lahadi 19 ga watan Maris.

KU KARANTA: Buhari aiki yake yi har cikin dare– Inji fadar shugaban kasa

Bala Lau yace duba da halin matsayin rayuwa da ake ciki, ya sanya kungiyarsu daukan wannan mataki na samar da cibiyoyin koyar da sana’a da suka danganci harkar noma da ayyukan hannu daban daban, don tallafa ma jama’a.

Lau yace sakamakon samun yawan mabiya da kungiyar take yi, wanda a cewarsa sun kai miliyan 20.

''Ya kamata mu samar ma matasan mu ayyukanyi musamman a fannin noma, sana’o’in hannu don su zama masu cin gashin kansu.

“A shirye muke mu kawar da mutanen mu daga kan titi da barace barace, wannan ne ya sanya muka dauki matakin samar da cibiyoyion koyar da harkokin nomad a sana’o’in hanu a duk fadin kasar nan.” Injji Bala Lau.

Shugaban Izala yace sun kafa kwamitin mutane 5 karkashin shugabancin Alhaji Mohammad Hassan kwamishinan kudi na jihar Gombe don samar da tsarin da za’a bi wajen cimma manufar da aka sanya a gaba.

“Muna da yakinin noma da sana’o’in hannu sune hanyoyi mafi saukin wajen samar da arziki a tsakanin mutane, musamman wajen kawar da matsin halin rayuwar da ake ciki a yanzu.”

Daga karshe Bala Lau yayi kira ga al’ummar musulmai dasu cigaba da yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a, da kasa baki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel