A fadawa Magu ya zo ya daure ni Inji wani Sanata

A fadawa Magu ya zo ya daure ni Inji wani Sanata

Jaridar Sahara Reporters ta tasa wani Sanata a gaba inda tace ashe bai kammala Jami’ar ba. Sai dai Sanatan ya maida martani yace ayi a gaji a kyale sa

Dino Melaye da Bukola Saraki

An fallasa wani Sanata ashe bai yi karatu ba

Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa Sanata Dino Melaye bai karasa karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba aka sallame sa. Sahara Reporters ta fitar da hotunan kwas-kwasan da Sanatan ya dauka inda aka nuna cewa ya fadi.

Sanatan ya mayar da martani inda yace sharri ne kurum ake masa. Melaye yace nan gaba ma ana iya cewa shi ba ‘Dan Najeriya bane. Sanata Melaye yace ba wannan bane karo na farko da Sahara Reporters tayi masa sharri.

KU KARANTA: Ashe Dino Melaye bai yi karatu ba?

Dino Melaye ya bayyana cewa yanzu haka yana karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariyar inda yake Digirin sa na 7. Sanatan yace a je a duba idan har karya ne a sa Magu na EFCC ya kama sa ya daure.

Kwanaki Sanata Dino Melaye yace dole fa sai dai shugaba Buhari ya turo wani amma ba Ibrahim Magu ba a matsayin wanda zai rike Hukumar EFCC don kuwa doka ba ta bada damar ayi ta aika sunan mutum daya ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel