Man Utd ta motsa bayan rabin shekara ana abu daya

Man Utd ta motsa bayan rabin shekara ana abu daya

– Man Utd ta bar matsayin da ta dade a Gasar Firimiya

– Kungiyar Man Utd ta koma na 5 a teburi

– Ita kuma Arsenal ta bar matakin da ta ke

Man Utd Cocah Jose Mourinho

Kocin Kungiyar Man Utd

Kungiyar Man Utd ta tashi daga mataki na 6 wanda ta dade a kai a wannan makon. Yanzu haka Man Utd ta dawo mataki na 5 inda ta kerewa Kungiyar Arsenal. Sai dai abubuwa na iya cabewa idan Man City da sauran manya suka ci wasannin su.

Man Utd dai tayi nasara ne bayan ta doke Kungiyar M/Boro da ci 3-1. Wannan ne kusan wasa na farko bayan Kungiyar M/Boro ta kori Kocin ta wanda tsohon Mataimakin Koci Jose Mourinho na Man Utd ne Aitor Karanka.

KU KARANTA: Asirin wana Miji ya tonu a Garin Kalaba

Marouane Fellaini da Dan wasa Smalling su ka jefa kwallaye a raga. Shi ma dai Dan wasa Jese Lingard ya zura kwallo mai kyau. Alvaro Negredo na Kungiyar Boro ne ya ci wa Kungiyar kwallo guda. Man Utd dai ta kai kusan watanni 6 a mataki na 6 a gasar firimiya.

Kwanaki Dan wasan bayan Kungiyar Man Utd Marcos Rojo ya tsaya cin ayaba yayin da ake wani wasa tsakanin Kungiyar ta Man Utd da Rostov na Gasar UEFA Europa League. Man Utd dai tayi nasara a wasan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel