Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Wata mata mai suna Chinasa Okereke tace wani yaro mai shekaru 15 ya amshi kwangilar samo ma wani Boka karamin yaro a kan N500, inda ya saci yaronta mai shekaru 3 ya mika ma bokan.

Chinasa ta bayyana haka ne ga manema labarai inda tayi zargin makwabcin tane ya sace mata yaro, sai dai kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ta ruwaito cewar yaron da ake zargin mai suna Simon ya tabbatar ma yansanda cewa wani boka ne ya aike shi ya samo mai karanin yaro mai shekaru 3.

Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Kayayyakin tsaf da aka gani a gidan

Simon yace bayan ya kawo yaron ne, sai bokan ya bashi N500 a matsayin kudin aiki, sai dai kash! Koda yansanda suka nufi gidan da aka kai karamin yaron, sai suka tarar da gawarsa kwance cikin jini.

Yayin da Chinasa ke bayani sai ta fashe da kuka, tana cewa ba wai tana jimamin yaronta bane kadai, yanzu haka a wasu mutane suna zuwa akan babur suna yin barazana ga rayuwarta dana mijinta, Augustine Okereke.

Chinasa tace yayanta hudu ne, da safiyar ranar da lamarin ya faru tana kokarin yi musu wanka ne, sai ta shiga daki don ta dauko zanin yafawa a jiki, kafin ta fito ne aka sace mata yaro, yayin data shiga nemansa, sai yarta mace ta bayyana mata cewa wai Simon ya tafi da shi.

KU KARANTA: An yi ragas, yayin da Uba da ɗa suka afka cikin rijiya, dukkansu suka mutu a jihar Sakkwato

“Da yarinyata ta fada min Simon ya tafi da Chigozie, sai na ruga zuwa gidansu, amma iyayensa suka ce ai suma suna nemansa, da yamma ta fara yi, sai muka kai kara ofishin yansanda. Daga nan ne yansanda suka shiga maganan.

“Ba tare da bata lokaci ba suka kama Simon, da aka kais hi ofishin yansanda sai ya fara bayani, kuma ya bayyana yadda bokan ya sanya shi samo masa karamiin yaro, kuma shine ma ya dauke su a motarsa, daga nan sai ya kai mu har gidan bokan, inda muka tsinci gawar Chigozie, an daure wuyarsa da jan kyalle.”

Chinasa ta cigaba da bayani: “Da aka tambaye Simon ta yaya bokan ya kashe Chigozie, sai yace a gabansa bokan ya daga chigozie sama, sai yayi wasu surutai, kawai sai Chigozie ya fado matacce.”

Kwamishinan yansandan jihar Legas Fatai Owoseni yace bokan yayi amfani da yaron ne wajen tsafi, sa’annan yace sun mika bokan zuwa sashin binciken manyan laifuka dake Yaba don cigaba da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel