Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Wasu dakarun rundunar sojan kasa dake karkashin bataliya ta 222 dake jibge a garin Agarha-Otor na karamar hukumar Ughelli sun daka wani lauya, har da karya masa gadon baya.

Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne aranar Asabar 11 ga watan Maris da misalin karfe 7 na yamma daidai lokacin da lauya Sunny Ekwe ya kai ma aminisa ziyara a a unguwar Okpara dake karamar hukumar Ethiope na jihar, sa’adda sojojin sun far masa.

KU KARANTA: Hirar ƙarshe da wani hafsan soja yayi da abokinsa kafin ýan Boko Haram su kashe shi

Bayanai sun nuna cewa sojojin sun jefar da lauyan a cikin kwata bayan sun lakada masa dan banzan duka.

Wata majiyar gani da ido ta shaida mana cewar lamarin ya samo asali ne a lokacin da sojoji suka nufo Ekwe, suka umarce shi daya biyo su zuwa wani waje, sai dai lauyan yaki yarda ya bisu, saboda yana tunanin tarkon rago suka shirya masa.

Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Rikicin lauyoyi da Sojoji: Sojoji sun karairaya wani lauya, tare da fasa masa ido

Sai dai hakan bai yi ma sojojin dadi ba, inda suka suka kira sauran sojojin, kafin kace kule! Sun fara casa shi. Wani abokin Ekwe ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka Ekwe na jinya a wani asibiti sakamakon raunuka daya samu a gadon bayansa, da idanunsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel