EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa tare da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta mika ma hukuma sojin sama wata katafariyar asibitin zamani wanda tsohon babban hafsan sojan sama Air Marshal Adesola Amosu ya gina da kudaden daya sace daga rundunar.

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

Jaridar Punch ta ruwaito cewar asibitin mai suna St.Solomon yana zaune ne a unguwar Adeniyi Jones dake Ikeja, birnin jihar Legas, kuma akwai kayayyakin aiki na zamani a cikinta, cikinsu har da wani na’urar daukan hoto data kai $1,000,000.

KU KARANTA: Buhari ya halarci Sallar Juma’a na farko tun bayan dawowarsa daga birnin Landan

Rahotannin sun bayyana cewar EFCC ta mika ma sojoji asibitin ne sakamakon ba zata iya tafiyar da shi ba,shi yasa suka mika ta ga rundunar sojan sama, tun da dai da kudin daya sata daga rundunar ne ya gina ta, zuwa lokacin da kotu zata kammala sauraron karar dake gabanta akan Amosu, hart a yanke hukunci, kamar yadda wata majiya ta shaida ma Punch.

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

Rahoton jaridar Punch din ta nuna cewar EFCC ta kwace kadarori da dama daga hannun Amosu da suka hada da wasu gidajen alfarma dake kan titin Adeyemo Alakija, GRA Ikeja wanda aka kiyasta kudinsa ya kai N250m; wnai gida a rukunin gidaje na Peace Court shima a GRA Ikeja da farashinsa ya kai N110m.

Bugu da kari, EFCC ta kwace ma Amosu wani gida da darajarsa ta kai N40m a rukunin gidajen rundunar sojin sama dake Asokoro Abuja, sai wani gida dake Fatakwal shima darajarsa ta kai N33m da kuma wani gida mai daraja N95m a layin Umaru Dikko, Jabi, Abuja. sa’annan gwamnati ta kammala shirye shiryen kwace wani katafaren gidan mallakn Amosu dake birnin Landan na pan miliyan 2.

EFCC ta mayar ma rundunar sojin sama wani katafaren asibiti da wani tsohon hafsan sojanta ya gina da kuɗin sata

Air Marshal Amosu

A wani hannun kuma, ma’aikata a ma’ikatan kula da harkokin kasar waje na cikin firgici da fargaba biyo bayan dirar EFCC ma’aikatan don gudanar da bincike kan dalilin daya sa aka sallami wani jami’in maikatan daya fallasa almundahana.

Rahotannin sun nuna cewar an sallami jami’in ne saboda ya fallasa wata badakalar satar $229,000 da kuma N800,000 wanda ake zargin jami’an ma’ikatan sun tafka. A yanzu haka fadar shugaban kasa ta umarci EFCC data bincike dalilin daya sanya ministan harkokin kasashen waje ya amince da sallamar jami’in.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel