Yan sanda sun dakatar da taron yan Shi’a

Yan sanda sun dakatar da taron yan Shi’a

Kungiyar musulman Shi'a sunyi Allah wadai da harin kwanan nan da kuma dakatar da taron addinin da suka shirya a Kano a ranar Asabar, sun bayyana hakan a matsayin yunkuri na tashin hankalin mambobin ta.

Yan sanda sun dakatar da taron yan Shi’a

Shugaban kungiyar Shi'a, Ibraheem Zakzaky

A cikin wata jawabi da sanya hannun kakakin kungiyar ta shi'a, Ibrahim Musa yace jami’an tsaro sun tarwatsa taron da sashin mata na kungiyar Shi’a suka shirya don tunawa da ranar haihuwar ‘yar mazan Allah, Fatima (amincin Allah ya tabbata a gare ta).

KU KARANTA KUMA: Hukumar NEMA ta shirya aiki bayan sabon harin da Boko Haram suka kai Borno

“Taron ya ya fara cikin kwanciyar hankali da misalin karfe 10 na safe, sai kawai wasu tawagar jami’an tsaro suka mamaye gurin taron bayan na safe don su tarwatsa ci gaban taron na rana, cewa an basu umurni daga Abuja kan su tarwatsa taron ta ko halin yaya” cewar jawabin.

Kungiyar ta zargi Gwamna Ganduje da bada umurnin kai harin, kamar yadda ya bayyana a kafar watsa labarai cewa zai yi duk abunda zai yi a karkashin ikonsa don kawo karshen yaduwar Shi'a a Kano.

A wani al’amari makamancin wannan, kungiyar tayi Allah wadai da harin da wasu yan iska suka kai ga mambobinta a Mariri, karamar hukumar Lere dake jihar Kaduna.

A cewar kungiyar, yan iskan sun mamaye gidan shugaban ta bayan sallar Juma’a a ranar Juma sannan suka jima yaran da suka rage a gidan raunuka.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel