Kungiyar gwamnonin kasa ta wanke kansu da sun bada nasu bangare kan labarin bashin kudi da kungiyar Faris-Landan suka bayar

Kungiyar gwamnonin kasa ta wanke kansu da sun bada nasu bangare kan labarin bashin kudi da kungiyar Faris-Landan suka bayar

- Sun kuma wanke kansu akan masu bada shawara da suka diba domin gane daidai kudin da za’a ba ma ko wani jihar

- Abin muhimmanci ne a fada cewar, an bi hanyoyin tafiyad da abu yadda ya kamata batun raba kudin daga farko har karshe

Kungiyar gwaminoni na Najeriya (NGF) sun wanke kansu da sun bada nasu bangare kan Labarin bashin kudi da kungiyar Faris-Landan suka bayar

Kungiyar gwaminoni na Najeriya (NGF) sun wanke kansu da sun bada nasu bangare kan Labarin bashin kudi da kungiyar Faris-Landan suka bayar

Gwamnonin Najeriya jiya sun bada nasu bangare na labarin cewar sun raba kudin da kungiyar Faris-Landan suka bama Najeriya domin taimaka wa jihohin kasar tsakanin su.

NGF sun tsaya akan cewar, tun da maganan ya taso a shekara 2005, ba su yi komai daya saɓa doka ba akai daga fari har karshen raba kudin.

Yadda NGF ta tsaya na cikin wani takarda da baban kafafen watsa labarai su, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fito da a Abuja, wai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gan irin darajan su gwamnoni ne ya sa aka fito musu da kudin da tun da dedewa na nan ba’a basu ba. Inji Bello wai an fito da kudin ne domin gwamnoni su samu na biyan albashin ma’aikata.

Ya kara cewar, idan shugaban kasa bai amince da gwaminonin ba, bai zai sa hannu a biya kudin na biyu ba, idan akwai alama na cin hanci.

KU KARANTA: Tab-di-Jan: Kashin Saraki da sauran manyan Majalisa ya bushe

NGF suka ce: “Gaskiya ne cewar, akwai dokoki da aka hada na bada kudin, amma anyi duka ne tare da izini gwaminoni kasar, ba wai an basu umarni kawai ba." Inji takardan, duk wannan ya faru ne domin an gano darajan gwaminonin.

Abin muhimmanci ne a fada cewar, an bi hanyoyin tafiyad da abu yadda ya kamata batun raba kudin daga farko har karshe, duk hukumomin da ya kamata daga ofishin ma'aikatar gwamnati na harkan kashe kudi, ofishin babban masu kirga kudi, Babban Bankin Najeriya, ofishin babban mai kula da harkar yadda aka kashe kudin da kuma majalisa.

Sun kuma wanke kansu akan masu bada shawara da suka diba domin gane daidai kudin da za’a ba ma ko wani jihar. Sun ce basu yi wannan ba domin satan kudi ko wani abu. Ko wani jihar suka kawo masu shawara amma daga baya aka hada su waje daya da wasu da basu kosa ba an bar su sun tafi. Wai yanzu haka, duk wayanan masu shawara da an dakatar da suna mike kai cewar, sun yi aiki akan maganan kudin.

Inji Bello: “Muna ganin maganan yan labari da suka ce kudin sun koma aljihun gwaminoni kamar maganan da ba hujja kuma ba dadi. Har yanzu, duk rahoton da ake fitarda, babu daya da ya nuna gwamna 1 da ya yi wannan laifi bare 7.

“Hukumar EFCC har yanzu na kan bincike amma basu samu komai ba tukun. Muna rokon masu labari su bi hanyar gaskiya wajen watsa labarai.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel