Hukumar NEMA ta shirya aiki bayan sabon harin da Boko Haram suka kai Borno

Hukumar NEMA ta shirya aiki bayan sabon harin da Boko Haram suka kai Borno

Wani hoto ya billo na abunda ya rage bayan tashin bam da ya afku a kauyen Ummarari a karamar hukumar Jere dake jihar Borno.

Hukumar NEMA ta shirya aiki bayan sabon harin da Boko Haram suka kai Borno

Kalli abunda ya rage bayan sabon harin Boko Haram a Borno

An rahoto cewa harin yayi sanadiyan rayukan wata uwa, ‘ya’yanta guda biyu da kuma wani mamba na kungiyar Civilian JTF. Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta bayyana.

A baya hukumar NAIJ.com ta ruwaito cewa al’amarin ya afku a daren ranar Asabar bayan musulmai sun idar da sallar Ishai.

Harin wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 7, sannan ya raunata mutane takwas.

A ranar Lahadi, Kakakin hukumar na agajin gaggawa ta kasa (NEMA) a yankin Arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim ya bayyana cewa an kwashe gawawwakin wadanda suka mutu sannan kuma an dauki wadanda suka ji rauni zuwa gurin da za’a basu kulawa.

Abdulkadir yace: “hukumar NEMA ERT da SEMA sun kwashi wadanda abun ya cika da su zuwa asibitin kwararru na jihar Borno.”

“An zuwa gawawwakin yan kunar bakin waken guda uku a dakin ajiye gawa dake asibitin.”

A halin da ake ciki, jami’an hukumar NEMA na Arewa maso gabas na a sansanin yan gudun hijira na Konduga don rarraba kayayyakin kwantar da hankali.

Hukumar NEMA ta shirya aiki bayan sabon harin da Boko Haram suka kai Borno

Kalli abunda ya rage bayan sabon harin Boko Haram a Borno

Kwanaki sansanin ya kama da wuta.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka rarraba masu sun hada da kayayyakin abinci, kayan aikin gida, kayan sawa, takalmi, tabarman leda da abincin yara.

An rarraba kayayyakin ne tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Borno BOSEMA son tabbatar da tsaron abinci.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

NAIJ.com
Mailfire view pixel