Sanata Ike Ekweremadu yayi babban gargadi

Sanata Ike Ekweremadu yayi babban gargadi

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya Ike Ekweremadu ya gargadi ‘Yan kasar inda yace har yanzu ba su yi hankali ba da darasin da ya faru a baya a kasar

Sanata Ike Ekweremadu yayi babban gargadi

Sanata Ike Ekweremadu da Mai gidan sa

Sanata Ike Ekwremadu yace jama’ar Najeriya ba su yi izna da abin da ya faru a lokacin yakin Biyafara ba inda aka yi mugun rashi a kasar. Ekweremadu yayi magana ne game da yadda abubuwa suke tabarbarewa a yankin Arewa ta gabas da rikicin Boko Haram ya fada masu.

Ekweremadu yace Majalisa za tayi bakin kokari wajen taimakawa inda rikici ya afka da su a kasar. Sanatan ya bayyana haka ne lokacin da tawagar Sarauniya Modupe Ozolua ta kai masa ziyara a Birnin Tarayya Abuja.

KU KARANTA: Sojoji za su fara daure Jama'a

Sanata Ike Ekweremadu yayi babban gargadi

Ekweremadu yayi babban gargadi game da barnar Boko Haram

Babban Sanatan ya tuna yadda abubuwa suka lalace a lokacin yakin basa-sa sannan yana karamin yaro. Yace idan ba a bi sannu ba Yankin Arewa da rikicin Boko Haram ya afka da su za su gamu da babbar matsala a kasar.

An gano cewa shugaban Majalisar dattawa da Mataimakin sa da kuma Kakakin Majalisar wakilai da mataimakin na sa sun saka haya ne a gidan da aka ba su. Kungiyar CSNAC mai yaki da cin hanci ta gano wannan don haka ma ta ke kira Hukumar EFCC ta damke shugabannin Majalisar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel