Tofa: Kashin su Bukola Saraki ya bushe

Tofa: Kashin su Bukola Saraki ya bushe

Shugabannin Majalisar Najeriya sun bada hayar gidajen da gwamnati ta ba su kamr dai yadda wata Kungiya mai suna CSNAC ta bankado

Tofa: Kashin su Bukola Saraki ya bushe

Tofa: Kashin su Bukola Saraki ya bushe

An gano wata sabuwar badakala a Majalisa inda aka bankado cewa ashe shugabannin Majalisa sun saka haya ne a cikin gidajen da Gwamnati ta ba su domin su karbi kudi. Yanzu haka dai an budowa manyan Majalisar wuta.

Kungiyar CSNAC mai yaki da cin hanci ta gano wannan don haka ma ta ke kira Hukumar EFCC ta damke shugabannin Majalisar. Shugaban wannan kungiya ta CSNAC Olanrewaju Suraju ya bayyana haka a wani bayani da ya sakawa hannu.

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC

Kwanakin baya dai Jaridar Sahara Reporters tayi bincike inda ta gano cewa shugabannin Majalisar dattawa da Kakakin Majalisar wakilai da Mataimakin sa sun saka haya ne a gidan da aka ba su. A haka dai Najeriya na asarar sama da Naira Miliyan 630.

Ranar Asabar ne Bukola Saraki ya bayyanawa wani gidan talabiji na TV Continential cewa ba saboda rahoton da DSS Majalisa ta ki tabbatar da Ibrahim Magu ba. Saraki yace Magu bai samu sa’a bane wajen tambayoyin da aka yi masa kamar yadda wasu kuma suka tsallake a baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel