Shirin 2019: Saraki ya fara ganawa da manyan Arewa

Shirin 2019: Saraki ya fara ganawa da manyan Arewa

Ba mamaki a cikin shirin 2019 ne har wasu ‘Yan siyasa sun fara kai ziyara wajen manyan Arewa. A jiya Bukola Saraki ya gana da tsohon shugaba Ibrahim Babangida

Saraki da IBB

Shirin 2019: Saraki ya fara ganawa da manyan Arewa

Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki ya fara ganawa da manyan Arewa wanda ba mamaki cikin shirin 2019 ne. A jiya ne dai Bukola Saraki ya tuntubi tsohon shugaba Ibrahim Badamasi Babangida watau IBB.

Ana dai tunani Bukola Saraki na harin kujerar shugaban kasa a wani karo mai zuwa, don haka ne ma ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB a gidan sa da ke Minna na Jihar Neja. Tuni dai dama har INEC ta bayyana ranar zabe na 2019.

KU KARANTA: Buhari aiki yake yi dare da rana

Bukola Saraki

Shirin 2019: Saraki ya fara ganawa da manyan Arewa

Sai dai ba mu san abin da Saraki ya tattauna da IBB ba, amma dai majiyar mu sun nuna mana cewa ba zai wuce maganar siyasa da 2019 ba. Nazari ya nuna cewa karshen abin da Bukola Saraki yake nema shi ne kujerar Muhammadu Buhari.

Kwanaki Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa yace akwai rikici tsakanin mutanen da ke zagaye da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sanatan yace dole sai shugaba Buhari ya bi a hankali da wadannan mutane na–kusa da shi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel