Ka wa gwamnatin tarraya hanyar dawo wa da N4bn kai ma ka samu N100m sakayya – Minista

Ka wa gwamnatin tarraya hanyar dawo wa da N4bn kai ma ka samu N100m sakayya – Minista

- Za’a kara daukan mataki ne bayan rahoton kwamiti da aka kafa akan yadda za samu abubuwa na gwamnati da suke hannu barayi

- An kafa kwamitin ne domin tsare mutane da za su rika hura kakaki nan gaba

- Duk mai hura kakaki da ya jawo bilyan N1 zai samu 5% na kudin. Sauran bilyan daya da ya aura kuma zai samu 4% akai

Ka wa gwamnatin tarraya hanyar dawo wa da N4bn kai ma ka samu N100m sakayya – Minista

Ka wa gwamnatin tarraya hanyar dawo wa da N4bn kai ma ka samu N100m sakayya – Minista

Gwamnatin tarraya ya dauki alƙawari zai mika milyan N100 wa duk wanda ya yi sanadiyar da aka samu karban kudi da ya ke bilyan N4 da wasu sun mallaka ta hanyar cin hanci.

Minista na labari da gargajiya, Alhaji Lai Mohammed ya kara tabbatar da wanan magana a takarda da aka fito da a jihar Legas ranar Ladi 19 ga watan Maris. Ya ce gwamnatin tarraya zai rufa ma kowaye da ya yi haka asiri.

Ya ce: “Akan wanda su samu damuwa garin labari da suka bayar, za’a duba maganan su , a kuma san abin yi akai.”

KU KARANTA: Ibrahim Magu : Majalisan dattawa ta aika wasika fadar shugaban kasa

Za’a kara daukan mataki ne bayan rahoton kwamiti da aka kafa akan yadda za samu abubuwa na gwamnati da suke hannu barayi. An kafa kwamitin ne domin tsare mutane da za su rika hura kakaki nan gaba. “Kar masu hura kakaki su ji tsoro, domin kwamitin sun hada hanyoyi da za’a bi domin karewan su. A gaskiya, sai dai su samu nasara, ba wai za su yi rashi ba,” inji ministan.

Ya kara cewa, duk mai hura kakaki da ya jawo bilyan N1 zai samu 5% na kudin. Sauran bilyan daya da ya aura kuma zai samu 4% akai; idan ya fi bilyan N5 kuma, zai samu 2.5% akai. “Misali, idan wani ya hura kakaki da za samu bilyan N10, zai samu 5% na bilyan N1, 4% kan na bilyan N4 da kuma 2.5% kan sauran bilyan N5 da suka rage.

“Abin da muka yi da wanan mataki shi ne, mu kara nuna wa mutane abin da za su samu kafin su ma hura kakakin,” ya tabbatar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel