Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau ya saki wani sabon bidiyo, wanda a ciki yayi barazana ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Duniya.

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

A cewar Abubakar Shekau a cikin bidiyon: "Buhari na tabbatar da cewa ka koyi darasi a yanzu. Lallai ka koyi darasin ka amma kana iya ci gaba a haka idan kana so. Amma fa ka tuna cewa babu wanda zai aikata mummunan aiki sannan kuma ya tsira."

"Da izinin Allah dukkan yaudaranka da karairayin da kake yi ma yan Najeriya na cewa kana yi masu aiki mai kyau ba zai kai ka ko ina ba. Bibbiyan sahun Amurka, Birtaniya ko kuma kace kana kammanta damokradiya da ilimantan da yara ilimin Boko ba zai yi maka amfani ba."

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

"Bazan yi maka fatan sharri ba amma zan bukace ka da ka nemi yafiyar Allah sannan ka tuba. Ka karbi ainahin koyarwan addinin musulunci ba wai ka dogara a kan azimi, sallah, zakka da hajji kawai ba."

"Abun ba a baki kawai yake ba domin addini ya kasance abunda ke koyarwan al-Qur’ani da dokokin ta. Bana so nayi magana da yawa. Shugaban kasa jumhuriyyar Nijar Muhammadu Yusufu kai makaryaci ne. ba ka is aka tsorata dalibai na ba sannan kuma idan na tashi a kan ka tunkara na zai yi maka wahala."

"Kawai ku dai tuna cewa idan dai zamu ci gaba da kasancewa musulmai kuma muyi aiki da koyarwar Al-Qur’ani zamu kasance masu karfi. Wannan ba abu da zaku iya wasa da shi bane. Ku daina cewa yan Boko Haram basu da aiki saboda farfagandan ku ba zai taimake ku ba a gaban Allah."

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

Sakon Abubakar Shekau ga shugaban kasa Buhari da sauran shugabannin duniya

"Wannan gargadi ne gare ku dukka. Don haka, wannan sako na yan uwana a musulunci ne don na tunasar da su kan ku ci gaba da sadaukar da kanku gurin gwagwarmaya. Ina tabbatar masu da cewa babu abunda zai kasakantar da gwagwarmayan."

"Mune muka tayar da dukkan bama-baman Maiduguri. Don haka bazamu taba hutawa ba har sai kun yarda da Al-Qur’ani."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel