Sarki ya bukaci da a cigaba da yi ma Buhari addu’a

Sarki ya bukaci da a cigaba da yi ma Buhari addu’a

Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari yayi kira ga yan Najeriya da su ci gaba da yima shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a, kan Allah ya bashi lafiya domin ya ci gaba da daukaka kasar Najeriya zuwa gaba.

Sarki ya bukaci da a cigaba da yi ma Buhari addu’a

Buhari na bukatar addu'an yan Najeriya

Sarkin yayi kiran ne a ranar Juma’a lokacin wani addu’a na musamman ga Buhari a babban massallacin Ilorin.

Magaji Nda na Ilorin, Alhaji Salisu Woru, ne ya wakilci basaraken a taron.

Gambari yace dukkan shugabanni Najeriya, imma shugaban kasa, Gwamna, Sanata ko dan majalisa ya cancanci addu’a akai-akai daga mutane kan Allah yayi masa jagora gurin tafiyar da gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Kin tantance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

“Shugaban kasa Buhari na aiki nagari don inganta kasar da dawo da ita kan hanya mafi inganci.

“Matslolin Najeriya ba gwamnati mai ci bace ta haddasa ta, dama chan suna nan, Buhari dai ya zo ne a lokacin da abubuwa suka birkice.

“Akwai bukatar muyi masa addu’an samun lafiya, samun jagorancin Allah, kariyan Ubangiji, ilimi da hikima gurin tafiyar da kasar,” cewar sa.

A baya, shugaban limaman Ilorin , Alhaji Mohammed Bashir, yayi addu’a ga Allah da ya ci gaba da ba shugaban kasa lafiya don ya ci gaba da shugabantar kasar sosai.

Shugaban ma’aikata, Alhaji Abdulwahab Babatunde ya wakilci Gwaman jihar, Dr Abdulfatah Ahmed, yayinda shugaban wani kungiyar siyasa na Ilorin, Abdullahi Issa ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel