Buhari ba zai iya kara turo mana sunan Magu ba – Dino Melaye

Buhari ba zai iya kara turo mana sunan Magu ba – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye yace dole fa sai dai shugaba Buhari ya turo wani amma ba Ibrahim Magu ba a matsayin wanda zai rike Hukumar EFCC

Buhari ba zai iya kara turo mana sunan Magu ba – Dino Melaye

Buhari ba zai iya kara turo mana sunan Magu ba – Dino Melaye

Sau biyu kenan Majalisa tana kin amincewa ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC mai yaki da sata a Najeriya. Wani Sanata yace yanzu dole sai dai shugaban kasa ya aiko sunan wani kuma dabam.

Sanata Dino Melaye yace babu yadda za ayi shugaba Buhari ya kara turo sunan Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC don kuwa akwai dokar Majalisa da ta haramta hakan. Melaye yace don haka Majalisa ba za ta kara la’akari da Magu ba a matsayin shugaban EFCC.

KU KARANTA: Ka ji abin da yasa Majalisa ta ki tabbatar da Magu

Dino Melaye ya kira shugaba Buhari ya aiko wani sabon mutum wanda ya san aiki ya kware, kuma mai ilmi da kamala. Dino Melaye mai wakiltar Yankin Jihar Kogi a Majalisar Dattawa yace Magu bai burge kowa ba yayin da ake masa tambayoyi wanda yace zai saba dokokin kasa idan aka kyale sa yayi aikin.

Bukola Saraki ya bayyanawa gidan wani talabiji na TV Continential cewa ba saboda rahoton da DSS ta bada Majalisa ta ki tabbatar da Ibrahim Magu ba. Saraki yace Magu bai samu sa’a bane wajen tambayoyin da aka yi masa kamar yadda wasu kuma suka tsallake a baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel