Goodluck Jonathan yayi kira ‘Yan siyasa su ji tsoron Allah

Goodluck Jonathan yayi kira ‘Yan siyasa su ji tsoron Allah

– Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kira ‘Yan siyasa su zama masu gaskiya

– Jonathan ya bayyana haka ne jiya a Jihar Ribas

– Goodluck Jonathan ya yabawa Gwamna Nyesom Wike

Goodluck Jonathan yayi kira ‘Yan siyasa su ji tsoron Allah

Jonathan yayi kira ‘Yan siyasa su ji tsoron Allah

Tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan Goodluck yayi kira ga ‘yan siyasar kasar da su zama masu gaskiya a duk inda su ke. Jonathan yace masu rike da mukamai su yi abin da ya dace a lokacin da suke kan mulki.

Jonathan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara Jihar Ribas inda ya gana da manema labarai. Jonathan ya kira masu rike da matsayi su dage wajen taimakawa talakawan su a ko da yaushe.

KU KARANTA: Tofa: Ga sako daga Abubakar Shekau

Goodluck Jonathan ya kuma yaba da irin aikin Gwamna Wike na Jihar Ribas din, inda Jonathan yace su na da kamanceceniya da Wike ta wani fanni musamman idan aka duba sha’anin kawo gyara ga al’umma.

Wani Tsohon Mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP na kasa watau Uche Secondus ya bayyana cewa PDP tayi wani babban kuskure a baya. Jam’iyyar PDP mai adawa ta furta cewa tayi babban kuskure wajen nada Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban ta ba tare da sani ba a cikin wancan makon da ya gabata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel