Shugaban kasar Ghana yayi abin da ba a taba yi ba a Afrika

Shugaban kasar Ghana yayi abin da ba a taba yi ba a Afrika

– Shugaban kasar Ghana ya kafa tarihi a kasar sa

– Sabon shugaban ya nada Ministoci 110

– Jama’a dai na ta kuka game da wannan lamarin

Shugaban kasar Ghana yayi abin da ba a taba yi ba a Afrika

Shugaban kasar Ghana yayi abin da ba a taba yi ba a Afrika

Sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya nada Ministoci sama da 100 a Gwamnatin sa. Shugaban dai yayi alkawari zai rage kashe kudin da Gwamnati take yi sai kuma ga shi ya kara yawan Ministocin kasar wanda yace ya zama dole ne domin ayi gyara.

Shugaba Nana ya nada mataimakan Ministoci har 50 tare da Ministocin Jihohi guda 4 bayan kuma dai ga asalin manyan Ministoci har guda 56. Hakan dai na nufin Ghana na da Ministoci har 110 kenan a yanzu wanda ba a taba yin hakan ba a tarihi.

KU KARANTA: Watakila Buhari ya kara albashin Ma'aikata

Shugaba Nana na Ghana

Shugaba Nana ya kara Ministoci 50

Jam’iyyar adawa dai ta soki wannan tsari inda kowane Minista yake da motoci da man fetur kyauta da kuma gida da masu gadi ga makudan albashi na akalla $4000 a kowane wata. Wasu Ma’aikatar dai akwai Ministoci har 5.

A Najeriya kuma Tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan Goodluck yayi kira ga ‘yan siyasar kasar da su zama masu gaskiya a duk inda su ke. Jonathan yace masu rike da makamai su yi abin da ya dace na taimakon talakawa a lokacin da suke kan mulki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan maganin Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel